rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Tarayyar Afrika Libya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sarkozy ya sake komawa ofishin yan Sanda

media
Tsohon Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy a kan hanyar zuwa ofishin yan Sanda. Kenzo TRIBOUILLARD / AFP

Tsohon Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya sake komawa ofishin yan sanda dake Nanterre domin ci gaba da amsa tambayoyi kan zargin da ake masa na karbar makudan kudi daga tsohon Shugaban Libya Muhammar Ghadafi domin yakin zaben sa.


Sarkozy ya kwashe yinin jiya ya na amsa tambayoyi daga yan sanda masu binciken cin hanci da rashawa da halata kudaden haramun.

Rahotanni sun ce Sarkozy ya bar ofishin ne da misalin karfe 12 na daren jiya talata kafin yau ya sake komawa ofishin dake Nanterre a Faransa.