Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojojin Najeriya 11 ne barayi suka kashe a jihar Kaduna

Majiyoyin labarai a Najeriya na cewa adadin sojojin kasar da suka rasa rayukansu sakamakon artabu da ‘yan bindiga da ake kyautata zaton cewa barayi ne ya kai sojoji 11 a kusa da Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

Sojojin Najeriya a cikin damarar yaki
Sojojin Najeriya a cikin damarar yaki REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Bayanai na nuni da cewa, wasu ‘yan bindiga ga alama magoya bayan shahrarren barawo kuma dan fashi da ake kira Buharin Daji ne suka yi wa sojojin kwanton bauna a wani cikin gandun dajin da ke tsakanin Birnin Gwari jihar Kaduna da kuma jihar Zamfara.

Makonni biyu da suka gabata ne aka bayar da labarin kashe Buharin Daji, wanda ya yi kaurin suna sakamakon jagorantar hare-hare domin satar shanu da kuma kisan jama’a a jihar Zamfara, lamarin da ya sa ake fassara harin da aka kai ranar talata kan sojojin a matsayin na daukar fansa.

Kawo yanzu dai ma'aikatar tsaron kasar ba ta ce komai ba dangane da wannan lamari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.