Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Sabbin takunkuman Amurka kan kamfanonin Sudan ta Kudu

Amurka ta sanya takunkumin cinikayya kan kamfanonin mai na kasar Sudan ta Kudu saboda zargin da ta ke yi musu na cewar suna taimakawa wajen iza wutar yakin basasar da ake yi a kasar.

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir REUTERS/Mohamed Nureldin Abdallah/File Photo
Talla

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Heather Nauert, ta ce daga yanzu duk wani kamfanin Amurka da ke shirin sayar wa kamfanonin man Sudan ta Kudu na’urori, sai ya nemi izinin hukumomin kasar kafin yin haka.

Jami’ar ta ce za’a sanya sunayen kamfanonin Sudan 15 da wannan takunkumi zai shafa.

Kakakin ma’aikatar wajen ta zargi wadannan kamfanoni da amfani da ribar da suke samu wajen sayan makamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.