Isa ga babban shafi
Faransa-Mali

Ana bukatar akalla shekaru 10 zuwa 15 domin tabbatar da tsaro a Mali

Ma’aikatar tsaron Faransa ta ce ana bukatar akalla shekaru 10 zuwa 15 kafin karshen yaki da kuma tabbatar da tsaro a kasar Mali sanarwa daga Janar Francois Lecontre Babban kwamandan askarawan Faransa.

Wasu daga cikin mayakan Azawad
Wasu daga cikin mayakan Azawad AFP/Stringer
Talla

Babban kwamandan askarawan Faransa na gabatar da jawabi ne a gaban Majalisar dokokin kasar,wadda ta gayyace shi domin yi ma ta karin bayani dangane da yadda yakin na kasar Mali ke gudana,

Janar Francois Lecontre ya ce akwai babban kalubale ga dakarun kasar ta Faransa da kuma sauran kasashe da ke aikin wanzar da tsaro a kasar ta Mali, kuma ana bukatar akalla shekaru 10 zuwa 15 domin samar da tsaro a kasar.

Babban kwamandan askarawan ya bayar da misali da sauran ayyukan wanzar da zaman lafiya a sassan duniya, da suka hada da Ivory Coast, yankin Balkans da kuma Afghanistan, inda dakarun kasa da kasa suka share tsawon shekaru kafin janyewarsu.

Yanzu haka dai Faransa na da dakaru sama da dubu hudu da ke yaki da ayyukan ta’addanci a yankin Sahel, wadanda aka tura sakamakon bullar kungiyoyin masu jihadi a 2013 a Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.