Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Boko Haram ta saki Leah Sharibu dalibar Dabchi da ta rage a hannunta

Kungiyar Boko Haram ta sako sauran yarinya daya da ta rage a hannunta daga cikin ‘Yan matan sakandiren Dabchi da suka dawo da su, inda rahotanni ke nuni da cewa yanzu haka tana kan hanyarta ta dawowa gida.

Wasu daga cikin daliban Dapchi kenan lokacin da ake sada su da mahaifansu kafin tafiya da su Abuja babban birnin Najeriya don basu kulawar lafiya.
Wasu daga cikin daliban Dapchi kenan lokacin da ake sada su da mahaifansu kafin tafiya da su Abuja babban birnin Najeriya don basu kulawar lafiya. REUTERS/Afolabi
Talla

A baya dai Boko Haram ta yi ikirarin cewa bazata saki Leah Sharibu ba har sai ta karbi addinin Islama.

Mahaifin Leah Sharibu Nathan ya bada tabbacin cewa Boko Haram ta sanar masa da cewa ‘yar tasa za ta dawo gida a yau Asabar kamar sauran rakwarorinta ‘yan matan na Dapchi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.