rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Saliyo

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotun kolin Saliyo ta dakatar da zaben makon gobe

media
Julius Maada Biyo,na Jam'iyyar SLPP da ke shirin karawa da Samura Kamara a zagaye na biyu na zaben shugabancin kasar da aka tsara gudanarwa a makon gobe. REUTERS/Olivia Acland

Kotun kolin kasar Saliyo ta bada umurnin dakatar da shirin zaben shugaban kasar zagaye na biyu da aka shirya yi ranar talata mai zuwa, saboda korafin da Jam’iyyar APC ta shigar a gaban ta.


Kotun ta umurci hukumar zaben kasar da ta jingine shirin gudanar da zaben zuwa ranar litini da zata yanke hukunci kan karar dake gaban ta.

Ana saran hukumar zaben ta gabatar da bayani kan zargin da ake mata, wanda kotun zata yi amfani da shi wajen yanke hukunci.

Julius Maada Biyo da Samura Kamara ne ake saran su fafata a zaben shugaban kasar zagaye na biyu.