rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An dakatar da zanga-zangar adawa da dokar haraji yau a Nijar

media
Wannan dai shi ne karon farko da kungiyoyin da ke yaki da dokar harajin suka bukaci gudanar da makamanciyar zanga-zangar. herald.ng

Hukumomi a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar sun haramta gudanar da wata zanga zangar da kungiyoyin fararen hular kasar suka shirya gudanarwa a yau lahadi. Zanga-zangar dai ci gaba ce kan wadda al'umma suka faro don nuna adawa da dokar haraji ta 2018 da gwamnatin kasar ta samar.

 


Haramta zanga-zangar dai a cewar hukumomin kasar ta biyo bayan rade-raden da ake da su na yiwuwar rashin tabbas kan tsaro a yankunan da aka shirya gudanar da zanga-zangar.

Rahotannin sun bayyana cewa yanzu haka jami'an 'yansandan Jamhuriyyar ta Nijar sun rufe ofishin kungiyar farar hula ta Alternative tare da kame shugabanta Musa Tchangari .

Kudirin gwamnatin ya bayyana cewa lura da irin wannan zanga zanga da kuma manufofinta ba za a iya tabbatar da tsaron ta ba.

Sudai kungiyoyin farar hular da ke yaki da dokar harajin ta 2018 a karon farko ke nan suka bukaci magoya bayansu da su fito zanga zangar tare da zaman dirshin a gaban Kofar ginin Majalisar dokokin kasar.