rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zimbabwe Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ana tuhumar Grace Mugabe kan safarar hauren-giwa

media
Uwargidan tsohon shugaban Zimbabwe, Grace Mugabe REUTERS/Philimon Bulawayo

'Yan Sanda a Zimbabwe na gudanar da bincike kan matar tsohon shugaban kasar, Robert Mugabe kan zargin da ake ma ta na safarar hauren giwa zuwa kasashen waje.


Rahotanni sun ce, Jami’an Kula da Gandun Dajin kasar sun mika wa 'yan sandan tarin bayanai dangane da yadda Grace Mugabe ta rika safarar hauren zuwa China da Daular Larabawa da kuma Amurka.

Kakakin 'yan sanda, Charity Charamba ta tabbatar da samun bayanan daga jami’an gandun dajin.

Christopher Mutsvangwa, jami’i a fadar shugaban kasar ya ce, wani jami’i ne ya tsegunta wa gwamnati labarin.