rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An kama mutane 23 da suka bijirewa doka a Nijar

media
Mohamed Bazoum Ministan cikin gida a Jamhuriyar Nijar AFP

Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun ce suna tsare da mutane 23 da aka kama saboda zanga zangar adawa da kasafin kudin bana wanda ya rikide ya zama tashin hankali.


Ministan cikin gida Bazoum Mohammed ya ce kama mutanen ya biyo bayan bijirewa dokar hana gudanar da zanga zangar, abinda ya kai su arangama da Yan Sanda.

Bazoum ya ce za’a cigaba da rufe gidan radiyo da talabijin na Ali Idrissa, saboda yadda ya dinga yada kalaman dake tinzira jama’a su shiga tashin hankali.