rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Saliyo

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotun Saliyo ta umarci ci gaba da zaben kasar

media
Za a ci gaba da zaben shugaban kasa a Saliyo bayan dakatar da shi saboda zargin magudin zabe REUTERS/Olivia Acland

Babbar Kotun Saliyo ta umarci Hukumar Zaben Kasar da ta ci gaba da gudanar da babban zaben kasar zagaye na biyu a yau Talata kamar yadda aka tsara duk da cewa hukumar ta bukaci karin kwanaki kalilan don kammala shirye-shirye, in da a yanzu ake saran gudanar da zaben a ranar 31 ga wannan wata na Maris.


Tun Asabar da ta gabata ne dai wata kotu da ke kasar ta hana yin zaben saboda karar da wani Lauya makusancin jam'iyya mai mulki ya shigar, in da yake zargin tafka magudi a zaben zagaye na farko.

Lauyoyin Hukumar Zaben Kasar sun janyo hankulan Kotu da cewa akwai hatsari domin an jefa zaben cikin rudani.

Mutane sama da 250 suka shiga cikin Kotun a yayin da take yanke hukunci jiya Litinin, ga kuma tsauraran matakan tsaro da aka dauka.

Jagoran adawa Julius Maada Bio na jam'iyar Sierra-Leone Peoples Party, SLPP ya yi rinjayen kuri'u da kashi 43%,  yayin da Samura Kamara na jam'iyya mai mulki wato APC ya samu kashi 42%  daga cikin jumullar kuri'u da aka kada a zagayen farko na zaben.

Rashin doke dan takarar adawa a zagayen farko ne dai ya sa ake ta fargaba da rade-radin rikici idan aka nemi yin magudi.

Kasar Saliyo dai ta fuskanci mummunan rikici da ya lakume rayukan mutane akalla dubu 50 a shekara ta 2002.