rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Liberia Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kawo karshen matsayi da ake baiwa yan Liberia a Amurka

media
Wasu daga cikin mutanen da suka cira a yakin kasar Liberia Financial Express

Shugaban Amurka Donald Trump ya bada umurnin kawo karshen wani matsayi na musamman da ake baiwa yan kasar Liberia dake zama a ciki da wajen kasar, saboda abinda ya kira ingantuwar yanayi a kasar da tayi fama da yakin basasa.


Fadar White House ta ce an daina yaki a kasar ta Liberia, kuma kasar ta samu cigaba da fannin demokradiya, saboda haka daga ranar 31 ga watan Maris na shekara mai zuwa dokar za ta soma aiki kamar dai yada fadar Shugaban Amurka ta tabbatar.

Tun shekarar 1991 yan kasar Liberia na da wata kariya ta musamman na zama a Amurka saboda halin da kasar su ta samu kan ta a ciki.