Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo

Mafi akasarin al'ummar Jamhuriyar Congo basa kaunar Kabila

Sakamakon wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a Jamhuriyar Congo, ya nuna cewa ‘yan kasar 8 daga cikin kowadanne 10, basa goyon bayan shugaban kasar Joseph Kabila.

Shugaban Jamhuriyar Congo Joseph Kabila.
Shugaban Jamhuriyar Congo Joseph Kabila. REUTERS/Kenny Katombe
Talla

Zalika kuri’ar ta nuna cewa ‘yan kasar 7 daga cikin kowadanne 10, basu da kwarin gwiwar zaben shugabancin kasar da za’a yi a ranar 23 ga watan Disambar wannan shekara zai zama sahihi, bayan shafe shekaru biyu da karewar wa’adin shugaba Kabila.

Al’ummar jamhuriyar Congo na cikin zullumin yadda zaben zai kaya, kasancewar har yanzu, babu wadda ya tantance kudurin shugaban kasar Joseph Kabila akan sauka daga mukaminsa, inda ake fargabar sake dage zaben.

Mutane da dama sun rasa rayukansu yayin zanga-zangar neman tilastawa Kabila yin Murabus a watannin baya, wadanda kungiyoyin kare hakkin dan adam suka zargin jami’an tsaron kasar da hallakawa ta hanyar amfani da karfi fiye da kima.

Rikicin siyasar kasar dai bada gudunmawa wajen kafuwar karin kungiyoyin ‘yan tawaye da kuma rikicin kabilanci musamman a gabashin kasar. Rikicin ya tilastawa dubban ‘yan kasar tserewa zuwa kasashen Rwanda da kuma Uganda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.