rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Saliyo

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Al'ummar Saliyo na zaben shugaban kasa zagaye na 2

media
Al'ummar Saliyo suna kada kuri'a a zaben shugaban kasar zagaye na biyo tsakanin Julius Maada Bio da Samura Kamara. REUTERS/Olivia Acland

A yau Asabar al’ummar kasar Saliyo ke kada kuri’a a zaben shugabancin kasar zagaye na biyu, wanda za’a fafata tsakanin dan takarar Jam’iyya mai mulkin kasar APC Samura Kamara da kuma jagoran ‘yan adawa na SLPP Julius Maada Bio.


An samu tsaikon gundanar da zagayen zaben na biyu ne, sakamakon karar da jam’iyyar mai mulki ta shigar bisa neman zargin an tafka magudi a zagayen farko da tayi rashin nasara a hannun Maada Bio, karar da kotu ta yi watsi da ita.

A zagayen farko na zaben dai dan takarar jam’iyyar adawa ta SLPP kuma tsohon shugaban mulkin sojin kasar Maada Bio ne ya samu kashi 43, yayinda Kamara ya samu kashi 42.

Sai dai tsarin zaben kasar Saliyo ya gindaya sharadin tilas dan takara ya lashe kalla kashi 55% na kuri’un da aka kada kafin darewa kujerar shugabancin kasar.

Dan takarar jam’iyya mulki ta SLPP Julius Maada Bio, ya taba shugabantar kasar Saliyo na gajeren lokaci, a yayinda suka hambarar da gwamnati a shekarar 1996, inda ya mulki kasar tsakanin watan Janairu na shekarar zuwa watan Maris.