Isa ga babban shafi
Saliyo

An rantsar da Bio a matsayin shugaban kasar Saliyo

Shugaban 'yan adawar kasar Saliyo, Julius Maado Bio ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi zagaye na biyu kamar yadda hukumar zabe ta sanar, bayan lashe kusan kashi 52 na kuri’un da aka kada, in da tuni ya sha rantsuwa a birnin Freetown.

Julius Maada Bio da ya lashe zaben shugaban kasar
Julius Maada Bio da ya lashe zaben shugaban kasar Reuters/Joe Penney
Talla

Hukumar zabe ta kasar Saliyo ta ce Julius Maada Bio, wanda tsohon soja ne, ya lashe kusan kashi 52 na kuri’un da aka kada, abin da ya ba shi nasarar doke Samura Kamara, dan takarar Jam’iyya mai mulki, wanda ya samu sama da kashi 48.

Sanar da sakamakon ya haifar da sowa da wake wake daga dubban magoya bayan Bio wadanda suka cika birnin Freetown jiya laraba.

Sanar da sakamakon keda wuya, shugaban alkalan kasar ya rantsar da Bio a matsayin zababen shugaban kasa.

Sai dai abokin takararsa, Samura Kamara ya bayyana rashin amincewarsa da sakamakon, in da ya ce, za su kalubalance shi a kotu, saboda abin da ya kira magudin da suka gano.

Sabon shugaban Bio na daga cikin wadanda suka yi juyin mulkin da ya kawo Valentine Stresser karagar mulki a shekarar 1992, lokacin yana da shekaru 25, daga bisani kuma ya karbe mulkin, amma kuma ya amince ya sauka a shekarar 1996 domin bai wa zababben shugaban kasa damar ci gaba da mulki, kana ya nemi gafarar al’ummar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.