rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Habasha Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Hukumomin Habasha sun saki wasu masu adawa da manufofinta

media
Abiy Ahmed,Firaministan Habasha a lokacin rantsar da shi REUTERS/Tiksa Negeri

Kasar Habasha ta saki wasu mutane 11 da ake tsare da su saboda adawa da gwamnati, cikin su harda yan jaridu da masu shafukan watsa labarai da jami’an kungiyoyin fararen hula.


Cikin wadanda aka sake harda dan Jarida Eskinder Nega da shugaban yan adawa Andualem Arage wanda a watan Fabarairu aka yiwa afuwa.

Sabon Firaministan kasar da aka rantsar ranar litinin ya bayyana aniyar sa na aiki tare da yan adawa da kuma kungiyoyin fararen hula.