Yan Bindiga a Gao sun kashe sojan Nijar
A kasar Mali wani sojan wanzar da zaman lafiya dan asalin Nijar ya rasa ran sa bayan wani harin ba zata da wasu yan bindiga suka kai a dai dai lokacin da ayarin motocin dakarun wanzar da zaman lafiya ke suture a garin Gao dake arewacin kasar ta Mali.
Wallafawa ranar:
Akala sojoji 100 ne aka bayyana mutuwar su a irin wadanan hare-hare daga yan bindiga da ake zaton mayakan kungiyoyin yan ta’addan arewacin Mali ne.
Shugaban rundunar wanzar da zaman lafiya a kasar ta Mali Mahamat Saleh Annadif mutuwar wannan soji asara ce ,musaman gani ta yadda wadanan yan bindiga ke ci gaba da kisan jami’an Minusma, Mahamat ya tabbatar da cewa hakan ba zai kawo masu cikas gay akin da suke yi da yan ta’adda a kasar ta Mali.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu