rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Saliyo

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Samura Kamara ya taya julius Maada Bio murnar lashe zaben Saliyo

media
Julius Maada Shugaban kasar Saliyo REUTERS/Olivia Acland

A kasar Saliyo, Samura Kamara tsohon Minista kuma dan takara a zaben shugabancin kasar ya taya Juluis Maada Bio murnar lashe zaben da ya gabata a jiya asabar.


Julius Maada da Kamara sun fafata a zagaye na biyu na zaben, wanda kuma Maada ya lashe da kusan kashi 52 na kuriu da aka kada.

Samura Kamara ya yi watsi da batun shigar da kara dangane da sakamakon zaben da hukumar zaben kasar ta bayar.

Sabon Shugaban kasar ta Saliyo Julius Maada Bio ya dau alkawalin aiwatar da sauyi na musaman a wannan kasa ta Saliyo tareda hadin guiwar sauran yan siyasa bangaren adawa da ma masu goyan bayan sa.