rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Rahotanni Nijar Amurka Sahel

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An fara wani atisayen sojin kasashe 26 a Nijar don yaki da ta'addanci

media
Kasashen da suke da wakilcin dakarun soji a atisayen na yaki da ta'addanci a Sahel sun hadar da 12 daga nahiyar Afrika da kuma 14 daga sauran sassan Duniya. REUTERS/Afolabi Sotunde

A safiyar yau ne aka kaddamarda bikin fara atisayen sojoji na hadin guiwar rundunar sojojin Kassashen waje, mai suna Flintlock kalkashin shirin Amurka. An gudanar da bikin ne a kalkashin jagorancin Jakadan Amurka da shugabannin rundunar sojojin Niger da Amurka da wasu karin kassashe 24, 12 na Afrika 14 na kassashen waje, gaba daya kassashe 26.Sojoji 1500 ne suka kasance a Niger domin samun horo na musamman akan hikimomi da dabarun yaki a yankunan da ta’addanci , saffarar muggan makamai, bil’adama da muyagun kwayoyi da ke barazana ga rayuwar al’umma. Ga rahoton wakiliyar Lydia Addo.


An fara wani atisayen sojin kasashe 26 a Nijar don yaki da ta'addanci 11/04/2018 - Daga Lydia Ado Saurare