Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko haram ta sace yara sama da 1,000

Majalisar dinkin Duniya ta bayyana cewar kungiyar boko haram ta sace yara sama da 1,000 a yankin arewa maso gabashin Najeriya daga shekarar 2013 zuwa yanzu, yayin da ta kashe malaman makaranta sama da 2,295.

Daliban Dapchi da kungiyar Boko Haram ta saki
Daliban Dapchi da kungiyar Boko Haram ta saki rfi hausa
Talla

Hukumar kula da kananan yara UNICEF ta majalisar tace kungiyar kan sace yaran ne domin sanya fargaba a tsakanin iyayen su, da kuma sauran jama’a.

Mohammed Malick Fall, jami’in hukumar a Najeriya, yace suna da alkaluman da suka nuna musu cewar kungiyar ta sace yara sama da 1,000, kuma adadin na iya fin haka.

Majalisar ta kuma ce kungiyar ta lalata makarantu sama da 1,400.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.