rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zimbabwe

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mugabe yaki ficewa daga gidan gwamnatin kasar

media
Robert Mugabe, tsohon Shugaban kasar Zimbabwe Phill Magakoe / AFP

Tsohon shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe yaki ficewa daga fadar shugaban kasa watanni biyar bayan kauda shi daga karagar mulkin kasar.


Mai magana da yawun fadar shugaban kasa, George Charamba yace har yanzu tsohon shugaban yaki kwahse kayan sa daga fadar shugaban kasa.

Charamba yace ba wai suna bukatar korar tsohon shugaban bane, amma dai bisa ka’ida ya dace a ce ya bar gidan tunda an samu sabon shugaban kasa.

Mugabe ya kwashe shekaru 37 yana jagorancin Zimbabwe har zuwa lokacin da ya’an jam’iyyar sa ta ZANU PF suka yi bore, suka kuma kauda shi daga mulki.