Adduo'i na karshe zuwa Winnie Mandela
Kusan jama’a dubu 40 ne suka halarci addu'o'in da aka yi a filin wasa na Soweto dake Johannesburg a Afirka ta kudu,in da suka yi ta wakokin jinjina ga Winnie Mandela wadda ta taka rawar gani wajen yakar mulkin wariyar launin fata a kasar.
Wallafawa ranar:
A yau asabar ake gudanar da zana’izar Winnie Madikizela Mandela,tsohuwar matar marigayi Nelson Mandela,wacce ta taka gagarumar rawa a yakin samarwa bakar fata inci a kasar.
Ana sa ran sama da mutane dubu 40 za su halara a babban filin wasa na Soweto dake Johannesburg don yi mata bankwana.
Winnie Mandela ta rasu ne ranar 2 ga watan Afrilun,ta na mai shekaru 81 a Duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu