Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Shekaru hudu da sace yan matan Chibok a Najeriya

Iyayen Daliban makarantar sakandaren Chibok da aka sace yau sun yi jerin gwano da addu’oi domin juyayin sace yaran su da kungiyar Boko Haram tayi shekaru 4 da suka gabata.

Wasu daga cikin daliban makarantar Chibok da aka ceto daga hannun kungiyar Boko Haram
Wasu daga cikin daliban makarantar Chibok da aka ceto daga hannun kungiyar Boko Haram REUTERS
Talla

Iyayen su maza da mata na daga cikin daruruwan mutanen da suka taru a makarantar sakandaren Chibok inda aka sace daliban 276 ranar 14 ga watan Afrilu na shekarar 2014.

57 daga cikin daliban sun samu kubucewa daga wadanda suka sace su, yayin da gwamnatin Najeriya tayi nasarar karbo sama da 100 daga cikin su, kana kungiyar na rike da sauran.

Sace daliban ya haifar da suka daga sassan Duniya, ciki harda rawar da jami’an tsaro ke takawa wajen kare lafiyar jama’ar dake yankin Arewa Maso gabashin Najeriya.

Ko a watan Fabarairu sanda kungiyar ta sake sace daliban makarantar sakandaren Dapchi 112, amma kuma akayi nasarar sako su gaba daya banda Leah Sharebu, wadda ita kadai ce krista a cikin su, saboda kin sauya addinin ta.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a sakon da ya aike na cika shekaru 4 da sace daliban, yace gwamnatin sa zata cigaba da kokarin ganin ta kubutar da sauran yan matan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.