Isa ga babban shafi
Najeriya

Majalisar Najeriya ta zargi gwamnati da sayen jirage ba da izininta ba

Majalisar dattijan Najeriya ta bukaci babban gwamnan bankin kasar da ministar kudi da na tsaro su gurfana gabanta don karin bayani kan wasu kudade da yawansu yakai dala milyan 162 da aka fitar don sayen makamai ba tare da shawarta ba.

Wani jirgi mai saukar ungulu
Wani jirgi mai saukar ungulu REUTERS/Tasnim News Agency
Talla

Sai dai kuma matakin Majalisar na zuwa ne a dai dai lokacin da kasar ke fafutukar sayo jiragen don kammala fatattakar ayyukan ta’addanci.

A cewar masana harakoki tsaro Air Kwamadan Tijjani Baba Gamawa ya bukaci a samu hadin kai domin samar da hanyoyin da suka dace tareda hadin gwiwar yan majalisa na Najeriya.

Rikicin Boko haram,kisan manoma da Fulani na daga cikin matsalolin da suka shafi rashin tsaro da ake fuskanta a tarrayar ta Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.