Isa ga babban shafi
Habasha

Majalisar ministocin Habasha zata soma aiki

Sabon Firaminstan Habasha, Abiy Ahmed ya nada sabon ministan tsaro a ci gaba da daukan matakin yi wa majalisar ministocinsa garanbawul don samun damar aiwatar da sauye-sauyen da al’ummar kasar suka bukata bayan jami’an tsaro sun kashe daruruwan mutane a wani rikici da ya barke a can baya.

Abiy Ahmed,Firaministan Habasha a lokacin rantsar da shi
Abiy Ahmed,Firaministan Habasha a lokacin rantsar da shi REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Abiy Hamed ya kuma nada sabbin ministoci 10, yayin da ya bar ministocin kudi da na harkokin kasashen waje da tsohon firaminista Hailemariam Desalegn ya nada.

A makon da ya gabata dai ne hukumomin Habasha suka saki wasu mutane 11 da ake tsare da su saboda adawa da gwamnati, cikin su harda yan jaridu da masu shafukan watsa labarai da jami’an kungiyoyin fararen hula.

Cikin wadanda aka sake harda dan Jarida Eskinder Nega da shugaban yan adawa Andualem Arage wanda a watan Fabarairu aka yiwa afuwa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.