Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

Shugaba Touadera ya nemi goyan bayan dakarun Afrika a kasar sa

Shugaban kasar Afrika ta tsakiya Faustin Archange Touadera ya sake jadada aniyar sa ta tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar ,a dai dai lokacin da wasu yan tsageru dauke da makamai suke kokarin rusa yanayin tsaro a wasu unguwanin babban birnin kasar Bangui.

Faustin-Archange Touadéra,Shugaban Afrika ta Tsakiya
Faustin-Archange Touadéra,Shugaban Afrika ta Tsakiya STRINGER / AFP
Talla

Yanzu haka dai al’umar babban birnin kasar Bangui na cikin zulumi,tun bayan da daya daga cikin kungiyoyin dake dauke da makamai da kuma keda cibiya a Kaga Bandoro suka yi barrazanar sa kai zuwa Bangui.

Dakarun wanzar da zaman lafiya a karkashin inuwar Kungiyar Afrika ta bayyana goyan bayan ta zuwa hukumomin kasar Afrika ta Tsakiya ,tareda sanar da bayar da tsaro da ya dace zuwa farraren hula.

Shugaban kasar ya bayyana cewa Gwamnatin na cikin shiri domin aikewa da jami’an tsaro zuwa wasu sassan kasar,a wani mataki na sake dawowa da doka da oda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.