Isa ga babban shafi
Madagascar

Zanga-zangar lumana ta zama tashin hankali a Madagascar

An kashe mutum 1 aka kuma jikkata wasu 16 a yayin barkewar rikici tsakanin masu zanga-zanga da jami’an tsaro a kasar Madagascar.

Zanga-zanga a birnin Paris na Faransa
Zanga-zanga a birnin Paris na Faransa REUTERS/Charles Platiau
Talla

An jikkata ‘yan jam’iyyar hamayya da dama a zanga-zangar da ta rikide ta zama tashin hankali tsakanin dubban masu fafutukar kare hakkin bil’adama da ke zanga-zanga da ‘yan sanda da jami’an Soji a kasar Madagaskar.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewar akalla dai mutane 5 ne aka jikakata a dauki-ba-dadin da ya faru a babban birnin kasar na Antananaribo.

Tun daga farko dai sai da mahukuntan kasar suka bayyana zanga-zangar a matsayin haramtacciya, amma ‘ya’yan jam’iyyar hamayya suka ki amincewa su dakatar da ita, suka kum aci gaba da zanga-zangar da ta haifar da tsananin rikici a ciki da wajen birnin Antananarivo.

Jami’an tsaro sun harba Barkonon Tsohuwa domin tarwatsa masu zanga-zangar, amma wasunsu sun maida martani ta hanyar jefa wa jami’an tsaron duwatsu.

Mai magana da yawun wata Assibiti ya shaidawa manema labarai cewar akalla sun yi wa mutane 11 da suka jikkata a yayin zanga-zangar jinya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.