Isa ga babban shafi
ECOWAS-CEDEAO

Sabon tsarin horar da jami'an kiwon lafiya na CEDEAO

Hukumar lafiya ta yankin yammacin Afrika ta kaddamar da wani shirin bayar da horo karo na farko zuwa jami’an kiwon lafiya 250 na kasashe shida domin yaki da mace-macen iyaye mata wajen haifuwa.Kasashen da za su morewa wannan sabon tsari sun hada da Nijar, Burkina Faso, Cote D’ivoire, Mali, Mauritania da Chadi.

Asibitin haifuwa a Jamhuriyar Nijar
Asibitin haifuwa a Jamhuriyar Nijar ©pixabay
Talla

Za a kwashe shekaru biyu ana bayar da horo zuwa jami’an kiwon lafiya a biranen Abidjan ,Yameh da Bamako da aka ware domin bayar da darusa zuwa likitocin da zasu fitowa daga kasashen.

Bincike daga hukumar lafiya ta Duniya na nuni cewa kasar Nijar ke sahun gaba wajen yawan mace-macen mata da yara a lokacin haifuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.