rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Kogi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An tabbatar da sakin Dino Melaye a Najeriya

media
Sanata Dino Melaye da ke wakiltar Kogi ta yamma a majalisar dattijan Najeriya. facebook

A Najeriya an tabbatar da sakin dan majalisar dattijai mai wakiltar jihar Kogi ta yamma a arewacin Najeriya wanda tun da farko aka kama shi lokacin da ya ke shirin Bulaguro zuwa kasar Morocco a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe a safiyar yau litinin.


Sanata Shehu Sani da ke wakiltar jihar Kaduna a majalisar Dattijan Najeriyar ya tabbatar da sakin Sanata Dino Melaye a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

A cikin watan da ya gabata ne ‘yan sanda suka bayyana Sanatan a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo bisa zargin sa da hannu a kisa da kuma bada goyon baya ga wasu bata-gari a jiharsa.