rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Lafiya WHO Ghana Malawi Kenya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Za a fara gwajin rigakafin cutar malaria a wasu kasashen Afrika

media
Wani likita yayin duba yaro da ya kamu da cutar malaria a wani asibiti da ke Arusha, a kasar Tanzania. Reuters

Hukumar kula da lafiya ta duniya WHO ta ce tana gaf da fara gwajin maganin rigakafin cutar cizon sauro a wasu kasashen nahiyar Afrika uku.


Kasashen sun hada da Kenya, Ghana da kuma Malawi, wadanda sune zasu zama na farko da zasu kafa wannan tarihi a Afrika.

Hukumar ta WHO da ke fatan ganin bayan cutar ta malaria a shekarar 2040, ta ce sama da mutane dubu 438 ne suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar a sassan duniya cikin shekara ta 2015.

Wani rahoton masana kiwon lafiya ya nuna cewa sama da mutane miliyan 200 ne suka kamu da cutar malaria a sassan duniya cikin shekarar da ta gabata.

Mafi akasarin wadanda suka kamu da cutar cizon sauron, sun fi yawa a nahiyar Afrika.