Isa ga babban shafi
Kamaru

An bukaci Majami'ar Katolika ta shiga tsakani a rikicin Kamaru

Kungiyar da ke yaki da tashe-tashen hankula da ake kira ICG ta bukaci Mujami’ar Katolika da ta shiga tsakani domin kawo karshen rikicin da kae samu a Arewacin Kamaru.

A cewar kungiyar Majami'ar ta Katolika na da ikon da za ta iya shiga tsakani don kawo karshen rikicin na Kamaru.
A cewar kungiyar Majami'ar ta Katolika na da ikon da za ta iya shiga tsakani don kawo karshen rikicin na Kamaru. RFI/ Pedro Costa Gomes
Talla

Wani rahotan da kungiyar ta fitar ya bukaci mujami’ar Katolikan da ta wuce gaba wajen sasanta rikicin na Kamaru wanda ke cigaba da haifar da rasa dimbin rayuka.

Kungiyar ta ce banda mujami’ar Katolika, kungiyoyi kadan ne ke da kimar shiga tsakani wajen sasanta irin wannan rikici domin kawo karshen sa ganin yadda lokacin zaben shugaban kasa ke karatowa.

ICG tace mujami’ar Katolika na da matukar kima a kasar ta Kamaru ganin dimbin magoya bayan da take da shi da kuma rashin goyan bayan wani bangare.

Rikicin na Kamaru ya fara ne a shekarar 2016, lokacin da matasan Yankin da ake amfani da Turancin Ingilishi suka fara neman ganin an basu damar taka rawa wajen harkokin yau da kullum a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.