Yammacin Afrika na fuskantar babbar barazana- MDD
Majalisar Dinkin Duniya ta ce Yankin Afirka ta Yamma na fuskantar babbar barazana sakamakon rikicin da ake samu tsakanin makiyaya da kuma manoma a sassa daban-daban.
Wallafawa ranar:
Wannan gargadi da Jakadan Majalisar Dinkin Duniya Mohammed ibn Chambas ya karanta a madadin Sakatare Janar Antonio Guterres ya zo ne lokacin bude taron kungiyar kasashen Afirka ta Yamma kan yadda za’a magance matsalar a Abuja.
Guterres ya bukaci daukar matakan gaggawa kan karuwar jama’a da sauyin yanayi da yaduwar makamai da kuma rashin aiwatar da dokokin Yankin da su ke kara matsalar.
Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osibanjo ya bukaci sake nazari kan dokokin ECOWAS domin shawo kan matsalar.
Shugaban gudanarwar kungiyar ta ECOWAS Jean-Claude Kassi Brou ya ce akalla shanu miliyan 60 ake da su a Yankin da ke bukatar wuraren kiwo wanda cigaban da aka samu ke haifar da rikice rikice.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu