rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Malawi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Joyce Banda ta koma gida Malawi

media
Dr Joyce Banda, tsohuwar Shugabar kasar Malawi Woodrow Wilson Center

Tsohuwar Shugabar kasar Malawi Joyce Banda ta koma gida bayan kwashe shekaru 4 da tayi tana gudun hijira na kashin kan ta sakamakon zargin da ake mata na cin hanci da rashawa.


Joyce Banda mai shekaru 68 ta gudu ta bar kasar ne bayan ta fadi zaben shekarar 2014, a daidai lokacin da ake zargin jami’an gwamnatin ta da sace miliyoyin daloli daga asusun gwamnati.

Daruruwan magoya bayan ta ne suka tare ta a tashar jiragen Blantyre, yayin da ta bayyana murnar ta da kuma aniyar komawa harkokin siyasa.

Mai magana da yawun ta Andekunye Chanthunya yace gobe lahadi ake sa ran ta halarci gangamin siyasa domin yin jawabi.