Barazanar Hukumomin Nijar na rufe gidajen abincin dalibai na kasar
Gwamantin Jamhuriyar Nijar tayi barazanar rufe daukacin shagunan sayar da kaya da kuma gidajen sayar da abinci dake cikin jami’oin kasar daga gobe litinin, muddin ba’a kawo karshen rikicin da ake samu a Jami’ar Yammai ba.
Wallafawa ranar:
Kakakin gwamnatin kasar Assoumana Malam Isa yace gwamnati ta damu da yadda dalibai ke kauracewa azuzuwa yayin da harkokin bada ilimi suka kankama.
Gwamnatin ta bukaci daliban da su koma cikin azuzuwan su domin karbar darasi daga gobe litinin ko kuma ta dauki matakan da suka dace.
Jamhuriyar Nijar na da jami’oi guda 8 dake dauke da dalibai 37,000, yayin da jami’ar Yammai ke da dalibai 23,000.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu