rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Madagascar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Dubban 'yan adawa suna zanga-zanga a Madagascar

media
Dubban 'yan adawa a kasar Madagascar, yayin zanga-zangar neman shugaban kasa a yayi murabsu a babban birnin kasar, Antananarivo. RIJASOLO / AFP

‘Yan adawa sama da dubu a kasar Madagascar sun ci gaba da gudanar da zanga-zanga a babban birnin kasar Antana-narivo kwanaki takwas a jere, inda suke neman tilastawa shugaban kasar, Hery Rajao-narimam-Pianina yayi murabus.


Zanga-zangar na zuwa ne, yayin da ya rage watanni bakwai a gudanar da zaben shugaban kasar da ‘yan majalisu, wanda ‘yan adawa ke zargin za’a tafka magudi a cikinsa.

Zalika ‘yan adawar suna zargin gwamnatin Rajao-Narimam-Pianina da yunkurin hana wasu manya adawa tsayawa takarar shugabacin kasar, ta hanyar kafa wasu sabbin dokokin zabe.

Zuwa yanzu mutane 2 suka mutu a zanga-zangaar, yayinda wasu 16 suka jikkata.