Isa ga babban shafi
Mali

Masu da'awar Jihadi su hallaka 'yan kabilar Tuareg 40

Gwamnan jihar Menaka da ke arewacin Mali Daouda Maiga, ya ce wasu mayaka da ke da’awar Jihadi, sun hallaka ‘yan kabilar Tuareg 40.

Wasu jami'an sojin kasar Mali, da suke sintiri a yankin Timbuktu.
Wasu jami'an sojin kasar Mali, da suke sintiri a yankin Timbuktu. Philippe Desmazes/AFP
Talla

Mafi akasarin wadanda aka hallaka matasa ne, kuma mayakan sa kai na kabilar ta Tuareg.

Rahotanni sun ce mayakan jihadin sun kai hare-haren ne har kashi biyu , a kauyukan Awakassa ranar Juma’a da kuma Anderan-Boucane a jiya Asabar.

Gwamnan jihar ya ce akwai yiwuwar mayakan sunyi amfani da rikicin ‘yan kabilar ta Tuareg ne da Fulani wajen samun damar kai harin.

Ci gaba da karuwar hare-haren a Mali dai babbar barazana ce ga shirin gwamnati na gudanar da zaben shugaban kasa, ta sanar da cewa za’a yi a cikin watan Yuli mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.