rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Madagascar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugaban Madagascar ya sanar da cewa ba zai sauka ba

media
Masu zanga-zanga a kasar Madagascar REUTERS/Clarel Faniry Rasoanaivo

Shugaban kasar Madagascar yace ba zai sauka daga mukamin sa ba duk da zanga zangar da yan adawa suka kwahse kwanaki 8 suna yi a kasar.


Yayin ganawa da manema labarai, shugaban Hery Rajaonarimampianina yace yana mulki ne da yawun miliyoyin al’ummar kasar da suka zabe shi, saboda haka sauka daga mukamin sa zai zama cin amanar su.

Yan adawan na zargin cewar gwamnati na shirin amincewa da wata sabuwar dokar zabe da zata hana su shiga, kuma tuni suka gabatar da korafin su a kotun fasalta tsarin mulki.