rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sabon tsarin samar da albarkatun gona a Nijar

media
Idrissa Moussa Kalla,daya daga cikin yan Nijar da suka koma noma da niyar bunkasa tattalin arzikin kasar rfi hausa

A Jamhuriyar Nijar ,da dama daga cikin yan kasar sun mayar da hankali zuwa hanyoyin samar da albarkatun gona kamar dai yadda Gwamnatin kasar ta bukaci ayi da shirin dan Nijar ya ciyar da dan Nijar.


Bayan da Manoma a wasu jihohin kasar suka bulo da wata sabuwar fasahar ta janyo ruwa daga rijiya ta hanyar amfani da Injina masu aiki da makamashin gas na girki ,

Wasu yan kasar sun dau niyar bunkasa noma dama kiwo ,wanda hakan ya taimaka sosai wajen samarwa matasa da ayyukan yi cikin dan karamin lokaci.

Elh Idrissa Moussa Kalla, daya daga cikin yan kasar da yanzu haka suka bulo da wannan shirin ,ya na mai fatan ganin yan kasar sun mayar da hankali zuwa noma da kiwo.