Isa ga babban shafi
Najeriya

Harin kunar bakin wake ya hallaka masallata a Mubi

Mutane da dama ake kyautata zaton sun mutu a wani harin kunar bakinn wake da ake zargin Boko Haram da kaddamarwa a wani masallaci da ke garin Mubin jihar Adamawa a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Wani kankanin Yaro ake zargi da tayar da bom din da ke jikinsa lokacin da ya shiga masallacin da ake tsaka da sallah.
Wani kankanin Yaro ake zargi da tayar da bom din da ke jikinsa lokacin da ya shiga masallacin da ake tsaka da sallah. REUTERS/Stringer
Talla

Lamarin ya faru ne a anguwar Wuro-Burode lokacin da al’umma ke tsaka da sallar Azahar.

Ko da ya ke dai har yanzu ba a kai ga tantance adadin mutanen da suka mutu ba, amma rahotanni sun adadin na da yawa ba ya ga wadanda suka jikkata.

Wasu shaidun gani da ido sun sanar da cewa wani karamin yaro ne daure da bom jikinsa ya shiga cikin masallacin tare da tayar da bom din.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.