Isa ga babban shafi
Najeriya

Fiye da mutane 60 sun hallaka a harin masallacin Mubi

Rahotanni daga Mubi da ke jihar Adamawa a yankin arewa maso gabashin Najeriya na cewa akalla mutane sama da 60 suka mutu sakamakon hare haren kunar bakin wake guda biyu da aka kai wani Masallachi lokacin Sallar Azahar. 

Wasu daga cikin wadanda suka jikkata kenan a harin da kungiyar boko Haram ta kaddamar.
Wasu daga cikin wadanda suka jikkata kenan a harin da kungiyar boko Haram ta kaddamar. REUTERS/Stringer
Talla

Harin wanda ake zargin kungiyar Boko Haram da kaddamarwa shaidun gani da Ido sun ce wani kankanin yaro ne ya tayar da bom din bayan da ya shiga sahun sallar da tsakarranar yau Talata.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito wani mazaunin garin Muhammadu Hamidu da yace da shi akayi janaizar mutane 68.

Bayanai sun ce wani dan kunar bakin wake ne ya kai harin da misalin karfe 1 na rana, lokacin ana kokarin Sallar azahar, yayin da daga bisani bam na biyu ya tashi.

Imam Garki, jami’in hukumar agajin gaggawa yace sun gano mutane 26 da suka rasa rayukan su a hadarin tare da jami’an Yan Sanda, yayin da aka ruga da 56 zuwa asibiti, kuma 11 daga cikin su raunin su yayi tsanani.

Gwamnatin Jihar Adamawa ta hannun kwamishinan yada labarai Ahmed Sajoh ta bukaci jama’a su bada gudumawar jinni domin taimakawa marasa lafiya.

Ko a watan Nuwamban bara ma makamancin harin a Mubi ya hallaka mutane da dama a Jihar ta Adamawa wadda ita ma ta yi kaurin suna wajen fuskantar hare-haren ta'addanci daga kungiyar ta Boko Haram kafin daga bisani a samu saukin lamarin.

Kawo yanzu dai babu kungiyar da ta dauki nauyin harin ko da ya ke kusan kowa na da yakinin Boko Haram ce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.