Isa ga babban shafi
Kamaru

'Yan aware sun sake hallaka jami'an tsaro a Kamaru

Wasu ‘yan bindiga a yankin da ake amfani da turancin Ingilishi, sun hallaka jami’an tsaro guda biyu a karshen mako.

Jami'an sojin kasar Kamaru yayin atasaye a garin Kolofata. Maris 16, 2016.
Jami'an sojin kasar Kamaru yayin atasaye a garin Kolofata. Maris 16, 2016. REUTERS/Joe Penney
Talla

Bayanai sun ce an kai hari kan Jandarmomin ne a Bali-Nyongha, ba tare da cikaken bayani akai ba.

Wani labari kuma yace an sace wani limamin darikar Katolika a Belo, na wani lokacin jiya litinin kafin daga bisani aka sake shi.

Bayanai sun ce limamin, William Neba yaki bin umurnin ‘yan awaren na daina karbar dalibai, abinda ya sa suka tsare shi.

A watan Oktoban bara ne, ‘yan awaren na Kamaru suka yi shelar ballewa tare da kafa kasar Ambazonia, matakin da yasa shugaban kasar, Paul Biya ya baiwa sojoji umarnin murkushe mayakan ‘yan awaren, kafa dokar hana zirga-zirga a yankunan kasar masu amfani da turancin Ingilishi.

Zuwa yanzu kimanin ‘yan kasar Kamaru 30,000 ne ke gudun hijira a tarayyar Najeriya, bayan tsrewa rikicin da suka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.