Isa ga babban shafi
Najeriya

An kara yawan Soji a Adamawa bayan harin Mubi da ya kashe mutane 86

Adadin mutanen da suka mutu a harin kunar bakin waken da kungiyar Boko Haram ta kai wani masallachi jiya a garin Mubin jihar Adamawa da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya ya haura 86.

Wasu tarin jami'an Sojin Najeriya kenan da ake shirin aika su Jihar Adamawa da ke yankin arewa maso gbashin kasar bayan fuskantar muggan hare-hare a baya-bayan nan.
Wasu tarin jami'an Sojin Najeriya kenan da ake shirin aika su Jihar Adamawa da ke yankin arewa maso gbashin kasar bayan fuskantar muggan hare-hare a baya-bayan nan. REUTERS/Stringer
Talla

Wani ganau a garin na Mubi ya shaida cewa da hannunsa sun binne mutane saba'in a jiya Talata, adadin da ya ninninka wanda hukumomin jihar suka bayar tun da farko, yayinda wani ma'aikacin makabarta ya ce basu kammala tantance adadin da aka binne a jiyan ba.

Rahotanni sun ce ko a safiyar yau sai da aka yi jana'izar akalla mutane 10 wadanda suka karasa mutuwa cikin dare sanadiyyar harin na jiya.

Tuni dai gwamnatin Najeriyar ta yi umarnin girke tarin jami'an tsaro a yankin na arewa maso gabashin kasar da ke fama da karancin tsaro.

Harin na Mubi dai shi ne mafi muni da kungiyar ta Boko haram ta kaddamar a baya-bayan nan da ya lakume tarin rayukan jama'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.