Isa ga babban shafi
Morocco

Morocco ta yanke alakar diflomasiyya da Iran

Kasar Morocco ta yanke dukkan huldar diflomasiya da kasar Iran, saboda zarginta da aikewa da makamai yankin Polisario dake jayayya da ita game da yammacin Sahara, wanda kowane bangare ke ikirarin mallakinsa ne.

Ministan harkokin waje na kasar Morocco  Nasser Bourita yayin jawabi ga zauren majalisar dinkin duniya, a watan Satumba, 2017.
Ministan harkokin waje na kasar Morocco Nasser Bourita yayin jawabi ga zauren majalisar dinkin duniya, a watan Satumba, 2017. REUTERS/Eduardo Munoz
Talla

Ministan harkokin waje na kasar Morocco Nasser Bourita, ya fadawa manema labarai cewa Iran ta aika da makaman ne ta jirgin ruwa, ta hannun wata kungiyar Hezbollah dake Lebanon, wadda ita kuma ta mikawa kungiyar ta Polisario mai samun goyon bayan Algeria da hadin gwiwar ofishin jakadancin Iran dake Algiers.

Ministan na Magana ne bayan da ya koma gida daga birnin Tehran inda ya fadi cewa ya shaidawa takwaransa na Iran Mohammed Javad Zarif matakin na Morocco.

Yankin na Polisario da kuma Morocco sun gwabza fada saboda neman mallakar yammacin Sahara a tsakanin shekarun 1975 zuwa 1991, inda Morocco ta karbe yankin kafin majalisar dinkin duniya ta shiga tsakani.

Morocco dai na daukar yankin yammacin sahara a matsayin nata.

A ranar Juma’a data gabata Kwamitin Sulhu na majalisar dinkin duniya, yayi kira ga Morocco da kungiyar Polisario da su shirya zaman tattaunawar sulhu a karkashin jagorancinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.