rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Algeria Nijar Bakin-haure

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Algeria ta taso keyar bakin haure fiye da 1500 zuwa Jamhuriyar Nijar

media
Yanzu haka akwai bakin haure sama da dubu uku da ke samun kulawa a cikin sansanonin hukumar ta OIM da ke garin Agadez arewacin Jamhuriyar Nijar. AFP PHOTO / MAHMUD TURKIA

Sama da mutane 1,500 ne kasar Algeria ta taso keyarsu zuwa jamhuriyar Nijar a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata a cikin yanayi mai kunci a cewar Majalisar Dinkin Duniya.Ko a kwanakin baya sai da Algeriyar ta mayar da wasu tarin bakin haure kasar ta Nijar duk da gargadin da ta yi mata na shigar mata da kowanne bakar fata ba tare da la'akari da kasar da ya fito ba.


Ofishin hukumar kula da bakin haure ta MDD a birnin Yamai fadar gwamnatin Jamhuriyar Nijar, ya ce 600 daga cikin wadannan mutane ‘yan asalin kasar Kamaru ne, yayin da sauran aka tantance su a matsayin ‘yan kasashen Mali da Guniea.

Mafi yawa daga cikin mutanen an jibge su ne a garin Asamakka, da ke gaf da kan iyakar Nijar da Algeria, kamar dai yadda shugaban ofishin hukumar ta OIM a jamhuriyar Nijar Guseppe Loprete ya tabbatar.

Wasu daga cikin mutanen da aka taso keyarsu, sun bayyana cewa bayan cafke su a sassa daban daban na Algeria, an tsare su a cikin mummnan yanayi, kafin daga bisani a kwaso su cikin manyan motoci zuwa iyakar da jamhur-yar Nijar.

Yanzu haka akwai bakin haure sama da dubu uku da ke samun kulawa a cikin sansanonin hukumar ta OIM da ke garin Agadez arewacin Jamhuriyar Nijar.