rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Muhammadu Buhari Amurka Birtaniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Buhari ya gaza komawa gida kwanaki 2 bayan barin Amurka

media
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. NAN

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gaza komawa gida kwanaki biyu bayan barinshi kasar Amurka inda ya gana da shugaban kasar Donald Trump, ganawar da ta kai ga kara dankon alakar da ke tsakanin kasashen biyu ta fuskar tsaro da kasuwanci.


A jiya Laraba ne dai al'ummar Najeriyar suka zuba idon isowar shugaban amma kuma kawo yanzu babu wasu bayanai kan isowar ta sa.

Sanarwar da mataimakin shugaban na musamman kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar ta ce yanzu haka shugaban na birnin London yayin da ya gaza tasowa saboda wasu matsaloli.

Tun farko dai fadar shugaban kasar ba ta sanar da cewa Muhammadu Buhari zai tsaya a birnin London bayan ganawa da Donald Trump a Amurka ba.

Bayan ganawa da Trump a ranar 29 ga watan Aprilu ne Muhammadu Buhari ya bar Washington ranar 1 ga watan Mayu inda guda daga cikin mataimakanshi kan harkokin yada labrai Bashir Ahmad ya ce shugaban na kan hanyar shi ta dawowa Najeriya, amma kuma kawo yanzu bayanai na nuni da cewa jirgin shugaban na birnin London.