Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Dr Jibril Ibrahim kan kalaman da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ke yi kan takarar Buhari a 2019

Wallafawa ranar:

A tarayyar Najeriya tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo na ci gaba da yin rubuce rubucen nuna suka ga shugaban kasar Mahamadu Buhari, da nufin ganin ya fadi a zaben shugabancin kasar na shekara ta 2019.A cikin wata sabuwar wasikar mayar da martini ga shugaba Buhari ga ya ce rubuce rubucen na Obasanjo zage zage ne da nuna kiyayaya karara a gare shi, tsohon shugaban kasar Obasanjon ya ce, marasa hankali da jahilai ne kawai ke goyan bayan Buharin. To domin jin raáyin masu sharhi a kasar kan wadannan wasiku da Obasanjo ke aikawa Buharin Mahaman Salisu Hamisu ya tattauna da Dr Jibrin Ibrahim ga kuma yadda firar ta kasance.

A baya-bayan nan dai tsohon shugaban Najeriyar na mummunar suka kan shugaba mai ci Muhammadu Buhari duk da cewa a baya yana daga cikin 'yan gaba-gaba da suka tsaya masa a takarar neman shugabancin kasar a 2015.
A baya-bayan nan dai tsohon shugaban Najeriyar na mummunar suka kan shugaba mai ci Muhammadu Buhari duk da cewa a baya yana daga cikin 'yan gaba-gaba da suka tsaya masa a takarar neman shugabancin kasar a 2015. AFP
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.