Isa ga babban shafi
Mali

'Yan ta'adda sun sake hallaka Azbinawa 16 a Mali

Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun hallaka Abzinawa 16 a arewacin kasar Mali, kwanaki kadan bayan kashe mutane 40 da akayi a wasu kauyukan kasar dake kusa da kan iyaka.

Wasu sojojin Mali Azbinawa yayinda suke sintiri a titunan garin Gao.
Wasu sojojin Mali Azbinawa yayinda suke sintiri a titunan garin Gao. AFP/Getty Images
Talla

Magajin Garin Menaka, Nanout, yace an kai harin ne daren ranar Talata a kauyen Tindibawen dake da nisan kilomita 160 daga Menaka dake kusa da iyakar Nijar.

Dan Majalisar karamar hukumar yankin Bajan Ag Hamatou, ya tababtar da mutuwar mutane 16 a harin.

Kafin harin na baya bayan nan, mayakan sa kai na Azbinawa sun bayyana cewa, mayakan ‘yan ta’addan sun yiwa wsu fararen hula 17 kisan gilla a matsayin hukunci, ciki harda tsofaffi, tare da kone gidajensu.

Hare-hare a kasar Mali sun karu a baya bayan nan, kasancewar mayaka masu da’awar jihadi da a baya suka fi karfi a arewacin kasar, a yansu sun bazu zuwa yammacin kasar, inda suke yin amfani da rikicin kabilanci tsakanin Fulani makiyaya da Azbinawa makiyaya wajen kai hare-hare.

Karuwar hare-haren dai babbar barazana ce ga kokarin da gwamnatin shugaba Ibrahim Boubacar Keita ke yi na zaben shugabancin kasar da aka shirya zai gudana a ranar 29 ga watan Yuli mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.