rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Cote d'Ivoire

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ana ci gaba da rage yawan sojoji a Cote D'Ivoire

media
Dakarun kasar Cote d'ivoire a birnin Abidjan SIA KAMBOU / AFP

Gwamnatin Cote d’ivoire na cigaba da rage yawan sojojin kasar domin rage adadin kudaden da kasar ke kashewa ta bangaren tsaro.


Kakakin gwamnatin kasar Bruno Kone, ya ce yanzu haka akwai wasu jami’an tsaro 2.168 da suka amince a sallame su daga aiki karkashin wannan shiri da gwamnatin ke kan aiwatarwa.

A jimilce dai kasar Cote D’Ivoire na da dakarun da yawansu ya kai dubu 25 cikin har da tsoffin ‘yan tawaye.

Matakin zai taimaka sosai wajen rage yawan kudaden da gwamnatin kasar ke kashewa a duk shekara.