rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Togo Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gwamnatin Togo ta musanta zargin karbar rashawa daga Bollore

media
Vincent Bolloré Shugaban kamfanin Bollore na kasar Faransa REUTERS/Charles Platiau

Karon farko Gwamnatin Togo ta musanta zargin da ake yi ma ta na karbar rashawa domin bai wa kamfanin Bollore na Faransa Kwangilar tafiyar da tashar jiragen ruwan birinin Lome


Ministan kwadagon kasar Togo Gilbert Bawara, ya ce ba wata hujjar da ke tabbatar da cewa an saba wa ka’ida wajen kulla yarjejeniya da kamfani Bollore,wanda ma’aikatar sharar’ar Faransa ke zargin da irin wannan badakala a kasar Guinee Conakry.

Kasar Togo na daya daga cikin kasashen dake huldar cinikaya da kamfanin Bollore na kasar Faransa,wanda akasari yake kula da bangaren tashar jiragen ruwa a Afrika.