rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Majalisa Najeriya ta yi watsi da kudirin bai wa maza hutun haihuwa

media
Zaman Majlisar Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde

Majalisar wakilan Najeriya da gagarumin rinjaye ta ki amincewa da bukatar kafa dokar da zata dinga baiwa mazaje damar tafiya hutu lokacin da matan su suka haihu, domin taimaka musu wajen yin jego.


Dan Majalisa Edward Pwajok daga Jihar Plateau ya gabatar da kudirin, inda ya bukaci bada hutun makwanni biyu ga mazajen domin renon jira jiran da aka haifa musu.

Bayan mahawarar da aka tafka, Majalisar wakilan da gagarumar rinjaye ta yi watsi da kudirin.