rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya BOKO HARAM Maiduguri

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mutane 7 sun mutu a harin kunar bakin wake yau a Maiduguri

media
Harin dai ya zo ne kwanaki kalilan bayan makamancinsa a jihar Adamawa wanda ya hallaka kusan mutane casa'in. Guardian Nigeria

Rundunar ‘yansandan jihar Borno ta tabbatar da harin kunar bakin waken da wasu mata suka kai wa wasu kauyuka a jihar. Harin na zuwa kwanaki kalilan bayan wani kazamin hari da Boko Haram ta kai masallaci a garin Mubin jihar Adamawa da ya hallaka mutane fiye da 90.


Kakakin rundunar DSP Edet Okon ya ce maharani mata ne guda hudu wadanda suka yi damara da bom a jikinsu suka tunkari kauyukan Mainari Kanuri da kuma Shua.

Sanarwar Rundunar ta ce ‘yan kunar bakin waken uku bom din da ke jikinsu ya tashi ne kafin su kai cikin jama’a yayinda dayar kuma ta tayar da bom din tare da hallaka wasu mutane 3 baya jikkata wasu 7.

Rundunar ta ce tuni ta mika gawakinsu ga babban asibitin birnin Maiduguri, yayinda wadanda suka jikkata kuma ke karbar kulawar gaggawa.